Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar China Yace Tsarin Gurguzu Ne Kadai Zai Ciyar Da Kasar Gaba


Shugaba Xi da wani babban jami'i
Shugaba Xi da wani babban jami'i

Mr. Xi ya kuma ayyana cewa duk wani yinkuri na raba Taiwan da kasar China tabbas zai wargaje, duk da ‘yancin cin gashi kan da tsibirin ke da shi.

Shugaban kasar China Xi Jinping ya yi amfani da kalaman kishin kasa masu karfi yau Talata a lokacin da yake jawabin rufe taron wakilan majalisar kasar.

Mr. Xi ya fadawa wakilan jam’iyyar NPC kusan su 3,000 cewa China na kan hanyar cigaba.

Ya ce tarihi ya nuna, kuma zai cigaba da nuna cewa tsarin gurguzu ne kadai zai iya cetar kasar, kuma sai ta hanyar mutunta, da habbaka akidun gurguzu na ‘yan China ne kadai kasar zata iya samun gagarumin sauyi.

Kafin a kammala taron, ‘yan majalisar dokokin kasar sun gabatar da kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar akan kawo karshen takaita wa’adin shugaban kasa da mataimakinsa, matakin da ya ba Xi damar cigaba da mulki har illa masha Allah.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG