Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Venezuela Ya Kira A Yi Zaben Kananan Hukumomi


Masu zanga zangar kin jinin Shugaban Venezuela Nikolas Maduro

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro yayi kira da a yi zaben kananan hukumomi, amma ba zaben shugaban kasa da wuri ba, wanda miliyoyin masu zanga zanga suke bukata.

Maduro ya kira abokan hamayya da su zo su zauna su saurari jawabinsa na mako da ya keyi a gidan talabijin.

An kara shirya wani gagarumin zanga zangar nuna kin goyon baya ga gwamnati a yau Litinin bayan munanan zanga zangar da ta afku a fadin kasar a farkon watan nan wacce tayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 20.

Masu zanga zangar suna kira ne da a yi sabon zaben shugaban kasa da wuri wanda ya kamata a yi shi shekara mai zuwa kuma suna bukatar Maduro da ya sauka daga kan mukaminsa. Amma gwamnati ta hana yin zaben shugaban kasa a wannnan shekarar.

Zanga zangar da ake gudanarwa kusan kullun ta barke ne sakamakon kokarin da Babban Kotun kolin kasar tayi na kwace karfin mulki daga hannun ‘yan adawa da suke da rinjaye a majalisar kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG