Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa


Bukola Saraki A Wata Tattaunawa Da Reuters

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki ya sanar da cewa zai tsaya takarar shugabancin Najeriya kasa da wata guda bayan ficewarsa daga jam'iyar APC mai mulki,

Saraki ya sanar da haka ne a wani zaman tattaunawar da ya yi da matasa karkashin tutar yunkurin zaburar da matasa su shiga takara da ake kira #NotTooYoungToRun , wanda aka gudanar a Otel din Sharaton dake birnin tarayya Abuja yau Alhamis.

An gudanar da taron ne da nufin tattaunawa kan yadda kamfen kungiyar matasan zata iya tsaida dan takarar shugaban kasa a zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara karkashin tutar wannan gangamin.

Bukola Saraki ya tattauna da matasa ‘yan siyasa da wadanda ke da sha’awar tsayawa takara a matakai dabam dabam.

A cikin jawabinsa kan halin da kasa ke ciki, Saraki ya bayyana cewa, “ana bukatar sabbin jinni su karbi ragamar shubancin Najeriya” Ya bayyana niyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da goma sha tara karkarashin tutar jam’iyar PDP, tare da bayyana cewa, ya hakikanta ya cancanci tsayawa takara kuma zai iya samar da ci gaban Najeriya da kuma ‘yan Najeriya.

Saraki ya bayyana cewa "kowanne dan kasa yana da ‘yancin samun dama a kuma rika damawa da shi, ko da daga wanne bangaren kasar ya fito ko kuma matsayinsa,. Ko da wanene kuwa ya kadawa kuri’a ko menene ra’ayinsa, tilas ne gwamnati ta yi maku aiki”

Yace yayi aiki a matakai dabam dabam da ya sami kwarewar shugabanci, da ya hada da aiki a majalisar dokoki da gwamnan jiha, yanzu kuma yana shugabancin majalisar dokokin kasa saboda haka yana da kwarewar da ake bukata na gabatar da sauye sauye da zasu kawo ci gaba na zahiri a rayuwar al’umma.

Yace “na san abinda ake bukata a samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki. Zan iya zartar da mawuyatan shawarwari idan bukata ta tashi. Zan jagoranci gabatar da ajandar da zata kawo canji a rayuwar talakawan Najeriya a cikin kankanen lokaci.”

Saraki ya bayyana cewa, ba za a ci gaba da yadda ake tafiya a halin yanzu ba, domin idan aka zabe shi shugaban kasa, gwamnatinsa zata yi aiki gadan gadan da zai sa Najeriya ta habaka cikin sauri. Ya kuma ce zai cika dukan alkawuran da suka shafi ci gaban ‘yan Najeriya.

Saraki ya buga a shafinsa na twitter cewa:

I have decided to answer the call of teeming youth who have asked me to run for President. Accordingly, I hereby announce my intention to run for the office of President of the Federal Republic of Nigeria

— Bukola Saraki (@bukolasaraki) 30 Agusta, 2018

Fita daga Jam’iyar PDP

Shugaban majalisar dattijan Bukola Saraki ya sanar da fita daga jam’iyar PDP ne a karshen watan Yuli bisa zargin wadansu kusoshin jam’iyar APC da rashin juriya. Da yake zayyana dalilansa na ficewa daga APC, Saraki yace, ya tsaida shawarar ficewa daga jam’iyar APC ne bayan ya yi kyakkyawar tuntuba..

Yace tsaida shawarar ficewa daga jam’iyar APC ba abu ne mai sauki ba, sai dai ya bayyana cewa ya tsaida wannan shawar ne bayanda ya yi iyakar kokarinsa duk da tsokanar da ya sha da muzantawa da kuma kuntatawa da ya rika fuskanta. Yace ya fice daga jam’iyar APC ne domin a sami zaman lafiya da sasantawa da kuma kyakkyawar dangantaka da juna.

An jima ana rade radin cewa, shugaban majalisar yana da burin tsayawa takarar shugaban kasa. Sai dai kafin sanarwar ta yau, bai fita fili ya bayyana wannan burin ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG