Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Riko Na Mali Yayi Jawabi Ga Kasa


Shugaban riko na Mali, Dioncounda Traore a hagu tare da shugaban ECOWAS, Alassane Ouattara na Ivory Coast
Shugaban riko na Mali, Dioncounda Traore a hagu tare da shugaban ECOWAS, Alassane Ouattara na Ivory Coast

Shugaban rikon na kasar Mali ya ce shugaba da firayim minista da ministocin gwamnatinsa, ba zasu tsaya takara a zaben da za a shirya ba

Shugaban riko na kasar Mali, Dioncounda Traore, ya bayyana shirye-shiryen yin garambawul ga gwamnatinsa, ya kuma nemi taimakon kasashen ketare wajen sake kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan kishin Islama.

A cikin jawabin da yayi ta telebijin ga al'ummar kasar a daren lahadi, Mr. Traore yace zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya mai mataimakan shugaban kaaa guda biyu har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe. Ya ce shugaban kasa, da firayim minista da sauran ministocin gwamnati ba za su shiga takarar wata kujera a zabubbukan da za a shirya ba.

Wannan jawabin shi ne na farko da yayi ga al'ummar kasar Mali tun ranar Jumma'a, lokacin da ya koma kasar daga jinyar da yayi a kasar Faransa. A watan Mayu ne 'yan zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati suka kutsa cikin fadar shugaban kasar, suka lakkada ma Mr. Traore duka a cikin ofishinsa.

A cikin jawabin nasa na lahadi, shugaban yace kasar Mali tana wani muhimmin gacci a rayuwarta.

A bayan wani juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 22 ga watan Maris, 'yan awaren kabilar Abzinawa da 'yan kishin Islama sun kwace yankin arewacin kasar. A cikin 'yan kwanakin nan, 'yan kishin addinin masu alaka da kungiyar al-Qa'ida, sun kara jaddada matsayinsu a sassan arewaci.

A kudancin kasar kuma, akwai damuwa a game da hadin kai da kuma kwanciyar hankali a cikin ita kanta gwamnatin rikon da kuma ikirarin cewa har yanzu sojojin da suka yi juyin mulki su na yin katsalanda a cikin harkokin gwamnati.

Ana sa ran cewa Mr. Traore zai nemi Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura wata tawagar sojojin kasashen waje domin ta taimaka wajen maido da oda a kasar Mali. Kungiyar ECOWAS ta ware sojoji kimanin dubu 3 da 300 domin girka su a kasar ta Mali.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG