Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Somalia Yace Sai Ya Rama


Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo

Shugaban Somalia, Mohamed Abdullahi Farmajo ya la’anci harin, da ya hallaka sojoji akalla 48 a ranar Alhamishin da ta gabata, wanda kuma wannan shine farmaki mafi muni da aka taba kaiwa akan duk wani sansani na sojan kasar.

Shugaban kuma ya aika da gaisuwar ta’azziya ga iyalan sojojin da aka hallakan.

Haka kuma shugaban yace gwamnatinsa zata taya hukumomin lardin Puntland wajen daukar fansa akan wannan harin.

Wannan alkawarin ya biyo bayan alwashin da shugaban yankin na Puntland Abdiweli Mohamed Ali ya sha ne, na cewa suma sun kaddamarda yaki gadan-gadan akan al-Shebab dake yankin na Galgala.

Mayakan na al-Shebab dai, wadanda suka afkawa barikin sojan daga kowace kusurwa, ance sun share kamar sa’oi suna fatattakar wurin da harbe-harbe kafin su kwace shi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG