Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan ta Kudu Ya Kira A Yafewa Tsohon Mataimakinsa Domin Zaman Lafiya


Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir

Yayinda suke shirin gudanar da wani babban taron jam'iyyar dake mulki a Sudan ta Kudu shugaban kasar ya bukaci 'yan jam'iyyarsa da su yafewa tsohon mataimakinsa da wasu jami'an dake gudun hijra waje su dawo gida domin kasar ta samu zaman lafiya

Yayin da ake tunkarar wani babban taro a Sudan ta Kudu a mako mai zuwa, shugaba Salva Kiir ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar SPLM mai mulki, da su yafewa tsohon mataimakinsa, Riek Machar, yana mai kiran da a bar shugaban ‘yan tawayen ya koma gida.

Shugaba Kiir, ya fadawa mambobin jam’iyarsa a lokacin wani taron da suka yi a makon da ya gabata a Juba cewa, “idan aka bar Riek Machar ya dawo Juba, na baku tabbacin cewa zan sa dakarun kasar nan su sama mai cikakken tsaro, idan kuma baku yarda ba, ai akwai dakarun hadin gwiwar yankin na RPF suna nan, za ku iya sa dakarun na RPF su ba shi tsaro.”

Shugaba Kiir ya kuma kara da cewa, yana so dukkanin mutanen da aka tsare a baya, ciki har da tsohon sakataren SPLM, Janar Pagan Amum, su koma Juba a karkashin matsayar nan ta zaman Lafiya da aka cimma ta Arusha a shekarar 2015 a Tanzania.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da shugabannin kasar ta Sudan ta Kudu za su cire girman kai, su yi aiki tare domin a ciyar da kasar gaba, yana mai cewa “ina bukatar mu duba irin halin kuncin rayuwa da mutanenmu suka shiga, sai mu sauya yadda ake tafiyar da al’amura.”

A wani labari mai nasaba da wannan, gwamnatin shugaba Trump ta ce za ta yi dubi kan irin tallafin da take bai wa kasar ta Sudan ta Kudu, tana mai nuna bacin ranta kan yadda aka gaza cimma matsayar zaman Lafiya domin kawo karshen tashin hankalin da kasar ke fuskanta.

Wata sanarwa da Amurkan ta fitar ta nuna cewa, kasar ta Amurkan, ta yi alfahri tare da nuna goyon baya a lokacin da Sudan ta Kudun ta samu ‘yancin kai a shekarar 2011, amma kuma ta dora laifi akan gwamnatin kasar, kan gazawa da ta yi na cimma muradunta.

Sanarwar ta kara da cewa, cikin shekaru bakwai, shugabannin kasar sun yi almubazzaranci da kudaden Sudan ta Kudu, sun kuma yi ta kashe mutanensu, tare da nuna rashin kwarewa da himma wajen ganin an kawo karshen yakin basasar kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG