Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Uganda Ya Haramta Sanya Riga Dake Hade Da Hula


Yoweri Museveni, shugaban kasar Uganda

Sanadiyar kashe wani dan majalisa Ibrahim Abariga da wasu suka yi ranar Juma'ar da ta gabata ya sa shugaban kasar Uganda haramta sanya riga dake hade da hula da ake kira hoodie a turance

A can kasar Uganda kuma, jiya Litinin shugaban kasar Yoweri Museveni ya bukaci a haramta amfani da rigunan nan da ke hade da hula da ake cewa hoodie da turanci kuma ya bukaci a Makala na’urorin bincike akan dukkan abubuwan hawa. Ya dauki wannan matakin ne biyo bayan kashe wani dan Majalisar a ranar Juma’a.

Kafofin yada labaru a yankin sun bada labarin cewa, a ranar Juma’a da maraice aka harbe Ibrahim Abariga wani dan Majalisa, a lokacinda aka yi zargin cewa wasu mahara sun yiwa motar sa kaca kaca da harsashe a lokacinda ya doshi gidansa dake kimamin kilomita goma daga baban birnin kasar. Haka shima mai tsaron lafiyar sa mai suna Sa’id Kongo Buga shima an kashe shi.

Shedun gani da ido sunce mahara biyu akan babur sanye da rigunan dake hade da hula suka tare motar dan Majalisar Abariga.

A wajen jana’izar Abariga jiya Litinin, shugaba Museveni cikin fushi yayi alkawarin cewa za’a gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin. Shugaban yayi kukar cewairin rigunan dake hade da hula na boye fuskokun mahara, al’amarin dake dagula gano, bata garin a saboda haka an haramta amfani da irin wadannan riguna a kasar.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG