Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban WHO Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Coronavirus Ke Sake Yaduwa a Turai Da Amurka


Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce hukumar na, a ta bakinsa, “matukar damuwa” da yadda cutar coronavirus ke ta yaduwa, musamman ma a Turai da Amurka.

Tedros Adhanon Ghebreyesus, ya gaya wa manema labarai jiya Litini, yayin hira da yakan yi da ‘yan jarida a birnin Geneva cewa, yaduwar coronavirus ta kai ma’aikatan jinya, abin da ya kira, “makura.”

Tedros ya dawo hedikwatar WHO jiya Litini a karo na farko, tun bayan da ya killace kansa na tsawon makonni biyu a matsayin kandagarki, bayan ya yi ma’amala da wani mai dauke da cutar.

Tedros ya kuma yi maraba lale da abin da ya kira, “labari mai karfafa gwiwa” game da rigakafin COVID-19, to amma ya yi gargadin cewa bai kamata mutane su yi sake ba, saboda kawai sanarwa a ranar Litini da kamfanin harhada magunguna na Moderna da ke Amurka ya yi.

Kamfanin ya ce rigakafinsa ya samu ingancin kashi 94.5 cikin 100 wajen yaki da cutar, bisa sakamakon wuccin gadi na mataki na uku da na karshe, na gwajin maganin a likitance.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG