Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Zimbabwe Yace za a Gudanar da Zaben Kasar Cikin Watanni Hudu Zuwa Biyar


Shugaban Zimbabwe-Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabwe-Emmerson Mnangagwa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa yace za a gudanar da zabe a kasar cikin watanni hudu zuwa biyar, wanda shine zai kasance na farko tun bayan hambare mulkin Robert Mugabe da ya dade bisa karagar mulki.

Mnangagwa ya yi alkawarin ne yayin ziyarar aiki da ya kai a Mozambique, bisa ga rahotanon da jaridar gwamnatin kasar Herald ta buga.

Ya yi alkawarin gudanar da zabe mai sahihanci domin ganin kasar ta shiga sahun kasashen duniya da ake gudanar da mulkin damokaradiya. Ana kyautata zaton gudanar da zaben cikin watan Yuli ko Agusta,

Tsohon shugaban kasar Mugabe dan shekaru casa’in da uku yayi mulkin Zimbabwe na tsawon shekaru talatin da bakwai kafin aka matsa mashi lamba ya yi murabus a watan Nuwamba bara, bayanda sojojin suka sauke shi daga mulki ya kuma rasa goyon bayan jam’iyarsa mai mulki ta ZANU-PF.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG