Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Addini da Gwamnati su Bankado Mutanen Boko Haram


Musulman Najeriya
Musulman Najeriya

Kungiyar cigaban al'ummomin arewa ta tsakiya ta bukaci shugabannin addinin Musulunci da Kirista su hada kai da gwamnati a gano mutanen dake kiran kansu Boko Haram da masu mara masu baya.

Kungiyar cigaban al'ummomin arewa ta tsakiya ta bukaci shugabannin addini da na gwamnati su hada kai su gano mutanen dake kiran kansu Boko Haram da wadanda ke bayansu.

Kungiyar ta bada gaskiya cewa hadin kan shugabannin shi ne kadai zai kaiga shawo kan ta'adancin da Boko Haram ta sa gaba da ma matsalolin da suka addabi Najeriya.

Shugaban kungiyar ta cigaban al'ummomin arewa ta tsakiya Mark Amani yace tun da yake masu kashe-kashen sun ce suna yi ne da sunan addini kamata yayi shugabannin addinan Musulunci da Kirista su hada kai da gwamnati wajen bankado batagari tsakanin mabiya addinan biyu ba wai batun kafa kwamitoci kawai ba. Yace idan ba za'a fito a gayawa juna gaskiya ba to yaudara ake yi. Yace tun farko kungiyar Boko Haram tace bukatarta ita ce ta ga an musuluntar da kowa a Najeriya. To sai dai akwai musulmai 'yan Boko Haram, akwai kiristoci 'yan Boko Haram akwai kuma matsafa 'yan Boko Haram domin sun samu hanyar yin kudi.

Kauce-kauce da rufa-rufa ba zasu taimaki kasar ba. Ya kamata shugaban musulmai da sarakunansu da na kirista su fito su kira al'ummominsu a yi magana da su. Yace kafa kwamiti ba zai yi tasiri ba. Kudi kawai ake kashewa akan banza. A rushe kwamitoci a fito a fuskanci gaskiya.

Hajiya Khadija Gambo Hawaja shugabar mata musulmi ta jihar Filato tace sun fito ne su nunawa duniya cewa abun da Boko Haram ke yi ba addinin musulunci ba ne. Yana yaki ne da Allah. Gwamnati ta gayawa duniya wanene Shekau. Tace ashirye suke su tayawa duk wanda zai yi fada da kungiyar.

Ga rahoton Zainab Babaji.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG