Accessibility links

Ganin gawarwakin 'yanuwansu sojoji da kungiyar Boko Haram ta hallaka yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga farautar yaran da kungiyar ta sace, wasu sun harzuka har ma sun yi harbe-harbe.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu dake Maiduguri babban birnin jihar Borno ya zanta da kakakin sojoji domin yayi karin haske daga bangarensu abun da ya faru.

Kanal Mohammed Dole mataimakin daraktan sadarwa na rundunar soja shiya ta bakwai dake Maiduguri yayi karin bayani bisa ga abubuwan da suka faru. Ya fara da cewa wasu jaridu da kafofin labaru sun fadi wasu abubuwa da ba daidai ba ne. Yace abun da ya faru shi ne lokacin da sojojinsu ke dawowa daga farautar yaran da aka sace sai aka yi masu kwantan bauna a hanya. An kashe wajen sojoji shida kuma wasu bakwai sun jikata.

Ranar Laraba aka kawosu asibiti inda likitoci suke kula dasu. Yayin da shugaban rundunar sojojin ya zo ya gansu da kuma ganin gawarwakin da ake gyarawa sojojin dake cikin bariki su ma sun nufi asibitin domin jajantawa. Ganin gawarwakin, sabili da jin tausayi da rashin jin dadi sai wasu sojojin suka harzuka har suka soma harbe-harbe a sama. Kanal Dole yace babu wanda ya ji ciwo sanadiyar hare-harben. Yace an kwantar da hankulan mutane kowa kuma ya koma bakin aikinsa.

Akan ko gaskiya ne an raunata kwamandan rundunar Janaral Ahmed Muhammed, Kanal Dole yace babu abun da ya sameshi ko na kusa dashi. Haka ma Kanal Dole ya musanta batun cewa sojojin sun nemi su kwana a wani kauye amma aka tilasta masu su koma Maiduguri cikin daren abun da ya sa 'yanuwasu suka harzuka.

Sai dai Kanal Dole ya tabbatar da cewa an canzawa kwamandansu wurin aiki kuma tuni wani yana rikon kwarya. Yanzu suna jiran wanda zai maye gurbinsa ne yayin da rundunar tsaro ta kasa ta sa a yi binciken lamarin.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
XS
SM
MD
LG