Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Eritrea da Habasha Sun Amince Su Gana


Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed da ministan harkokin wajen Eritrea Osman Saleh Mohammed a hannun dama yayin ziyarsu zuwa Addis Ababa

Da alama dangantakar diflomasiya zata dawo tsakanin Eritrea da Habasha kasashe biyu dake makwaftaka da juna da suka kawashe shekara 20 suna zaman tankiya amma yanzu sun amince su gana

Shugabannin kasashen Habasha da Eritrea sun amince su gana a karo na farko cikin shekaru 20, wanda wata alama ce ta cigaba a diflomasiyyance tsakanin kasashen arewa maso gabashin Afirka makwabtan juna.

Ministan Harkokin Wajen Habasha Workneh Gebeyehu ya gaya ma kamfanin dilancin labarun Associated Press jiya Alhamis cewa ganawar za ta samar da "wata dama ta maido da zaman lafiya." Ya kara da cewa amma har yanzu ba a tantance lokaci da kuma wuri ba.

Babban jami'in na diflomasiyyar kasar Habasha ya yi wannan maganar ce a daidai lokacin da tawagar kasar Eritrea, karkashin jagorancin Ministan Harkokin Wajen Kasar Osman Saleh ke kammala wata muhimmiyar ziyara ta tsawon kwanaki uku a Habashar.

Kasashen biyu sun katse huldarsu bayan da yaki ya barke tsakaninsu sanadiyyar takaddamar kan iyaka a 1998, shekaru biyar bayan da Eritrea ta samu 'yancin kai daga Habasha.

Ganar za ta kasance haduwa tsakanin Shugaban Habasha mai kokarin sauye-sauye, Dr. Abiy Ahmed da kuma Shugaban Eritrea Isaias Afwerki, shugaban daya daga cikin kasashen da su ka fi ware kansu a duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG