Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Manyan Jami'an Eritrea Ta Isa Habasha


Firai Ministan Habasha ya tarbi tawagar Eritrea
Firai Ministan Habasha ya tarbi tawagar Eritrea

A karon farko tun daga lokacin da suka gwabza yaki biyo bayan ballewar Eritrea daga Habasha, tawagar manyan jami'an Eritrea ta isa Addis Ababa babban birnin Habasha domin tattaunawa bisa nufin Firai Ministan Habasha na kawo karshen rikici tsakaninsu

Wata tawagar manyan jami’ai daga Eritrea ta isa makwabciyarta Habasha domin fara wata tattaunawa mai cike da tarihi a kan kawo karshen daya daga cikin yaki mafi dadewa a Afrika.


Tawagar ta Eritrea ta isa birnin Addis Ababa ne a jiya Talata.


A makon da ya gabata ne shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya yi alkawarin aikewa da tawagar, a lokacin da kasarsa take bukin tuna mazan jiya a babban birnin kasar Asmara. Alkawarin na shugaba Afwerki wani martani ne ga alkawarin da Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed ya yi a farkon wannan wata cewa zai mutunta ka’idodin yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2000 domin kawo karshen yakin shekaru biyu a kan iyakokin kasashen.


Habasha ta dade bata amince da ka’idodin yarjejeniyar ba, da ta hada da janyewar Habasha daga garin Badme dake kan iyaka.


Eritrea tsohon lardi a cikin Habasha, ta balle ne a shekarar 1993.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG