Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Rasha da Turkiya Sunce Kashe Jakadan Rasha Ba Zai Bata Zumuncinsu Ba


Mutumn da ya kashe jakadan Rasha dake Turkiya
Mutumn da ya kashe jakadan Rasha dake Turkiya

Shugabannin Rasha da na Turkiya sun ce kisan da aka yiwa jakadan Rasha a Turkiya ba zai bata zumuncin dake tsakanin kasashen biyu ba.

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya bada tabbacin cewakasashen biyu na da ra’ayi iri daya da shugaba Vladimir Putin na Rasha gameda al’amarin Syria, kuma huldarsu ba zata huskanci wani kalubala a sakamakon wannan harin ba.

Shugaban Turkiya ya fadi hakan ne bayan wata hira ta waya da yayi da takwaransa na Rasha da yammacin shekaranjiya Litinin, a cewar kampanin dillancin labarai ta Faransa.

Ministocin harkokin waje na kasashen biyu sun ajiye huranni a gaban hoton marigayi jakadan Rasha din, Andrei Karlov a birnin Moscow.

Wani dan sanda ne ya harbe Jakadan na Rasha kuma ya kashe shi a don nuna jin haushinsa da rawar da Rasha ke takawa a yakin Syria.

Gawar Karlov ta isa birnin Moscow ne a jiya Talata tare da matarsa.

XS
SM
MD
LG