Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabar Mexico Ta Sanar Da Kakaba Harajin Ramuwar Gayya Kan Amurka


Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum yayin taron manema labarai da ta kira a fadar domin sanar da martani da mayar kan haraji da Trump ya kakaba wa Mexico
Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum yayin taron manema labarai da ta kira a fadar domin sanar da martani da mayar kan haraji da Trump ya kakaba wa Mexico

Sheinbaum ta kuma zargi Washington da wallafa sanarwar batanci da bata mata suna ba tare da wata hujja ba

Mexico za ta mayar da martani akan harajin da Shugaba Donald Trump ya kakaba mata da haraji makamantan hakan, kamar yadda Shugaba Claudia Sheinbaum ta bayyana a yau Talata, inda ta zargi Washington da kokarin batawa gwamnatinta suna.

Babu wani dalilin da zai sa Trump ya kakabawa kayan Mexico harajin kaso 25 cikin 100 duk da hadin kan da take baiwa kokarin yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, kamar yadda ta bayyana a wani taron manema labarai a yau da safe.

"A yau ina son in fayyace cewar a koda yaushe zamu nemi maslaha ta hanyar tattaunawa kamar yadda muka gabatar a bisa mutunta diyaucinmu," a cewar Sheinbaum.

Sai dai shawarar da Amurka ta yi gaban kanta wajen dauka ya shafi kamfanonin cikin gida da na ketare da ke aiki a kasarmu kuma ta shafi al'ummarmu. Don haka, mun yanke shawarar mayar da martani ta hanyar matakan da suka shafi haraji da wadanda basu shafesu ba," kamar yadda tace, inda ta kara da cewar za'a fitar da karin bayani akansu anan gaba.

Sheinbaum ta kuma zargi Washington da wallafa sanarwar batanci da bata mata suna ba tare da wata hujja ba," bayan da a sanarwarta ta karin harajin, fadar White House ta yi zargin cewar gwamnatin Mexico na bada mafaka ga manyan masu fataucin miyagun kwayoyi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG