Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shuwagabannin Kasashen Afrika Na Bukatar Mutunta Demokaradiyya


A yau Laraba 2 ga watan Oktoba tsofafin shuwagabannin kasashen Afirka suka fara gudanar da wani taro a birnin Yamai a jamhuriyar Nijar, karkashin inuwar cibiyar bunkasa dimokradiyya ta kasar Amurka NDI.

An gudanar da taron da nufin nazarin hanyoyin karfafa matakan mutunta wa’adin mulkin shuwagabannin kasashe dai dai da yadda yake rubuce a kundin tsarin mulki.

Mutunta kundin tsarin mulki, da yin biyayya ga ka’idar da ta kayyade wa’adin mulki a wajen shugabannin, wani abu ne da binciken cibiyar National Democratic Institute ta gano, cewa ya matukar taimaka wajen kaucewa barkewar tashe tashen hankula masu nasaba da hayaniyar siyasa a kasashe da dama.

Tsohon shugaban kasar Benin Nicephore Soglo, daya daga cikin jagororin wannan taron ya bayyana fatan ganin wannan taro, ya kasance wata hanyar karfafa mulkin demokradiyya a Afirka, don ganin anan gaba a fara mika mulki a hannun wanda talakawa suka zaba, ba tare da wata hatsaniya ba.

Shugaban kungiyar CEDEAO Issouhou Mahamadou na Nijar, da ya jagoranci bukin bude wannan taro, ya sake nanata cewa zai mutunta kundin tsarin mulki a karshen wa’adin mulkinsa na biyu, na karshe. Saboda haka burinsa shine ya damka mulki a hannun wanda ya lashe zabe a shekarar 2021.

Tsofaffin shuwagabannin kasashe 5 ne suka halarci wannan taro, wadanda suka hada da Goodluck Jonathan na Najeriya, Caterine Samba Panza ta RCA, Nicephore Soglo na Benin, Amos Sawyer na Liberia, da kuma Alhaji Mahaman Ousman na Nijar, wanda ya bayyana mana mahimancin wannan haduwa.

A jibi Juma’a ne za'a kammala wannan taro dake samun halartar ‘yan rajin kare dimokradiyya da dama, a karkashin gayyatar cibiyar bunkasa demokrdiyya ta kasar Amurka NDI, da kungiyar farar hula ta OSIWA mai ofishi a kasar Senegal.

Ga cikakken rahoton wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG