Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Simon Lalong Ya Yi Alkawarin Kawo Sauyi A Jihar Filato


Gwamnan jihar Plato Simon Lalong
Gwamnan jihar Plato Simon Lalong

Al’ummar jihar Filato sun bayyana fatar gwamnan jahar Simon Lalong zai aiwatar da tsare tsare da zasu kawo ci gaban jahar. Al’ummar jihar sun bayyana hakan ne a hira da suka yi da sashen Hausa na Muryar Amurka.

Biyo bayan rantsuwar kama aiki da gwamnan jahar Filato Simon Lalong ya yi na ci gaba da shugabancin jihar karo na biyu, wasu al’ummar jihar sun bayyana fatar samun sauyi masu inganci da zasu kyautata rayuwar su.

Babban batu da yafi dauke hankalin mutane Filato shine batun baiwa matsa aiki yi domin dogaro da kai. Sai batun batun ilimi da inganta karatu ta yanda matasa ba zasu dogara da ayyukan gwamnati ba, su iya kafa sana’o’i domin taimakawa kawunan su kuma hakan zai sa a samu saukin tashe tashen hankula a jihar.

Shiko gwamnan jihar Filato, a hira sa da Muryar Amurka a kwanakin baya, ya yi bayani a kan abubuwan da zai fuskanta a mulkin sa karo na biyu, da suka hada da biyan albashin ma’aikata da samar da tsaro ga al’ummar jihar.

Shima gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar wanda ma’abucin jihar Pilato ne yace yana da yakinin Simon Lalong zai samar da sauye-sauye masu inganci a jahar.

Wakiliyar mu a Filato Zainab Babaji ta shirya mana wannan rahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG