Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Najeriya Sun Yi Watsi Da Rahoton Amnesty


Manjo Janar Chris Olukolade

Rundunar sojin Najeriya ta yi fatali da rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adama da Amnesty International ta fitar da ke cewa ta yiwa fararen hula dubu bakwai kisan gilla a cikin shekarun da ta kwashe ta na yaki da Boko Haram.

Da yake wa taron manema labarai jawabi a Abuja mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade ya bayyana rahoton na Amnesty International a matsayin kage ne kawai ga dakarun kasar.

‘’Abin bakin ciki shine kungiyar da bata taba yin Allah waddai da ta’addanci ba a Najeriya yanzu take ikrarin wai ta yi bincike mai zurfi .” Inji Olukolade

Ya kara da cewa a fili ya ke kungiyar ta Amnesty na yin kazar-kazar ne kadai wajen gabatar da zarge-zarge mara ma’ana.

“A da lokacin da yan ta’ada ke samun koma baya abin bakin ciki ne Amnesty International na amfani da wannan rahoton domin muradin ta da ake kokwantansa da yakin da ake yi da ta’addanci’’

Olukolade ya kuma ce ya yi takaicin yadda kungiyar ke yin gum da bakin ta yayin da masu ta da kayar baya ke cin Karen su babu babbaka.

Idan Zaa iya tunawa ita dai Amnesty International ta fidda wani rahoto inda a ciki take bayyana yadda sojojin Najeriya ke wa fararen hulla kisan gilla, har ma ta bayyana sunayen wasu manyan hafsoshi da kuma rundunar mayakar kasar na da hannu wajen tafka wannan aika-aikan.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:33 0:00

XS
SM
MD
LG