Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arangama tsakanin Sojoji da ‘yan Boko Haram


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Wasu da ake zata ‘yan kumgiyar Boko Haram ne sun kai hare kan garin Borote, da ke karamar hukumar Biu dake jihar Borno.

Wasu da ake zata ‘yan kumgiyar Boko Haram ne sun kai hare kan garin Borote, da ke karamar hukumar Biu dake jihar Borno, inda suka kona wata makarantar Firamare, suka kuma raunana Sojoji uku.

Wannan hari dai yazo ne bayan kwana daya da wasu jami’an soja suka kaiwa wadannan ‘yan bindigan hari a wani gari da ake kira Kawuri a karamar hukumar Kwanduga, inda suka hallaka ‘yan bindiga fiye da hamsin, da kuma kwato makamai masu yawa.

Bayanai dake fitowa daga garin Borote na nuni da cewa ‘yan bindiga da dama sun gamu da ajalinsu, sakamakon gaba da gaba da suka yi da dakarun Sojojin Najeriya.

Duk da irin wannan nasaran da jami’an tsaron suka samu jama’a da daman na ci gaba da tserewa daga kauyuka zuwa manyan biranai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG