Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Mayakan Sama Sun Rugurguza Wasu Sansanonin 'Yan Boko Haram


Jirgin yaki dake sarafa kansa da kansa, wato bashi da matuki

Rundunar sojoji mayakan saman Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda take ikirarin yiwa kungiyar Boko Haram mummunar hasara a wani sansaninsu dake cikin dajin Sambisa

Sanarwa dake dauke da sa hannun daraktan rundunar mai hulda da jama'a Air Commodore Dele Alonge tace hare-haren da jiragen yakin suka dinga kaiwa ba kama hannun yaro cikin 'yan kwanakin nan sun lalata wuraren da 'yan Boko Haram ke gyara motocinsu da rumbunan makamai da na manfetur.

Air Commodore Alonge yace munanan hare haren sun kara samarda yiwuwar kawar da 'yan Boko Haram daga yankin arewa maso gabas cikin gaggawa. Rundunar tace tana anfani da jiragen leken asiri masu sarafa kansu da kuma wani iri daban.

Hafsan sojin Najeriya mai murabus Aliko El-Rashid ya yi tsokaci akan lamarin dake faruwa.

Yace matakin da mayakan sama suka dauka yana da tasiri domin zai kawowa 'yan Boko Haram koma baya. To amma akwai matsala. Aliko yace duk matakan ba zasu kaiga kawar da 'yan ta'adan ba. Sai an hada da wasu dabaru kafin a shawo kansu.

Wuraren da sojojin suka lalata yanzu ba su kadai ba ne 'yan ta'adan suke dashi. Suna da wasu a wasu sakon da ba'a sani ba.

Aliko yace koda an yi nasara a dajin Sambisa akwai sauran rina a kaba. Ya ambaci wurare uku da 'yan Boko Haram suka koma bayan sun bar dajin Sambisa. Saboda haka sojojin sama da na kasa ba zasu iya kawo karshen ta'adancin 'yan Boko Haram ba. Matakan na iya takaita abubuwan da suke yi amma ba zasu kawo karshensu ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG