Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Na Tuna Zagoyawar Barkewar Cutar COVID-19


Tedros Adhanom Ghebreyesus
Tedros Adhanom Ghebreyesus

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO, tana bukin zagayowar shekara da ta ayyana dokar ta bace ta kiwon lafiyar jama’a ta kasa da kasa, sakamakon barkewar cutar COVID-19, ta hanyar kira ga kasashen duniya su dauki kwararan matakan dakile yaduwar annobar.

A jiya Juma’a a wani taron da hukumar ta saba yi a helkwatarta a Geneva, babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce a shekarar da ta gabata a ranar Asabar, adadin kamuwa da cutar bai kai guda dari ba kana babu wanda ya mutu da cutar a wajen China.

A cikin makon nan, mutane da suka kamu da cutar sun haura miliyan dari kana mace mace ya tasar ma miliyan guda da dubu dari biyu. Tedros ya fada cewa, a waccan lokaci ya gargadi duniya cewa akwai damar dakile yaduwar cutar. Ya kara da cewa wasu kasashe sun dauki shawarwarin wasu kuma sun ki dauka.

Tedros ya ce allurar rigakafi da aka samu a yanzu ta sake baiwa duniya wata dama ta kawo karshen wannan annoba, kana ya ce bai kamaci a yi warwason rigakafin ba, a raba ta daidai wa-deda tsakanin kasashe masu arziki da talakawa.

Tedros ya kalubalanci abin da ya kira da masu kishin samar da rigakafi, yana nuni da batun boye rigakafin da wasu manyan kasashen duniya ke yi yanzu, yayin da kasashe matalauta ke zaman jira allurar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG