Accessibility links

Sojoji Sun Kashe 'Yan Bindiga 9, Suka Kama Sauran Biyun A Tudunwada, A Jihar Kano


An kuma kama makamai da albarusai har da kwamfuta tare da sauran mutane 2 da suka rage da rai daga 'yan bindigar

Sojoji a Jihar Kano dake arewacin Najeriya sun yi kwanton-bauna suka hallaka 'yan bindiga guda 9, suka kama saura guda biyun da suka rage da rai a kan hanyar Tudun Wada.

A cikin daren jiya talata zuwa asubahin yau laraba ne 'yan bindiga suka kai farmaki a kan ofishin 'yan sanda da banki da kuma gidan jami'in 'yan sanda a garin na Tudun Wada. Da sojoji suka samu labari, sai suka tare hanyar suka yi musu kwanton-bauna, inda aka yi musanyar wuta.

A bayan sauran 'yan bindiga guda biyu da aka kama, an kuma samu makamai da albarusai da yawa har ma da kwamfuta a motocin mutanen.

Birgediya-janar Iliyasu Abba, yayi ma 'yan jarida bayanin yadda wannan al'amari ya faru....

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG