Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Gano Masana'antar Bam Ta 'Yan Boko Haram A Kano


Bama-baman da aka fara hadawa cikin durom, da bindigogi da albarusai da aka gano yayin da sojoji suka kai sumame kan wani gida dake Sabuwar gandu a yankin Kumbotso.

Bam ya tashi ya kashe mutane biyu, ya raunata sojoji biyu, aka kuma kama mata 4 da yara 8 a wannan gida dake Sabuwar Gandu a Karamar Hukumar Kumbotso ta Kano

Bam ya tashi ya hallaka wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar nan ce ta Boko Haram, ya kuma raunata sojoji biyu a cikin daren nan da ya shige, a lokacin da wasu zaratan sojoji na Najeriya suka kai sumame kan wani gida a Sabuwar Gandu dake yankin karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Hukumomin soja a Kano, sun kuma ce an kama mata guda 4 da yara kanana su 8 a cikin gidan, a bayan da mazajen dake cikinsa suka tayar da bam cikin wata mota a lokacin da sojoji suka yi kokarin kutsawa cikin wannan gida.

Haka kuma, an samu durom-durom wadanda ake kokarin maida su bama-bamai a cikin gidan.

Kwamandan runduna ta 3 ta sojojin Najeriya a Kano, Birgediya Janar Iliyasu Isa Abba, ya zagaya da manema labarai wannan gida dake Sabuwar Gandu, inda suka ganewa idanunsu wannan wuri, kamar yadda za a iya gani cikin wadannan hotuna dake kasa, za a kuma iya jin bayani a sama a gefen dama.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG