Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kubatar Da Mutane Daga Sambisa


Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

A cigaba da yakin da sojojin Najeriya keyi da 'yan ta'adan Boko Haram, rundunar soji ta bakawai dake Maiduguri ta samu nasarar kubuto wasu mutane da dama daga dajin Sambisa

Mutanen da sojojin suka kubuto sun hada da mata da maza da kuma tsoffi a wasu kauyuka dake dajin yankin Sambisa.

Kwamandan shiyar Manjo Janar Lucky Irabor ya shaidawa manema labarai cewa rundunar tasu ta hallaka wasu 'yan Boko Haram su goma sha uku da kuma kama wasu da dama. Saidai sun rasa nasu sojojin guda biyu sakamakon barin wuta da suka dinga yi da maharan. Haka kuma soji daya ya jikata yana kuma karbar magani a asibiti.

Rundunar ta kuma kwato wasu shanu kusan dari uku. Tuni sun mikawa masu shanun. Sun kuma kama wani dake samarwa 'yan Boko Haram din man fetur da wasu kayan bukatau irin na yau da kullum..

A ranar uku na wanna watan ne sojojin suka kubutar da wasu mutane a wani kauyen Walasa cikinsu har da 'yan Kamaru guda biyu. Janar Irabor yace yana son 'yan Najeriya su sani sojoji zasu kakkabe duk 'yan Boko Haram dake dajin Sambisa. Ga 'yan Boko Haram da suka ajiye makamansu suka mika kansu Janar Irabor yace zasu karbesu bisa dokar kasa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG