Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Musanta Yunkurin Juyin Mulki a Lesotho


Firai Ministan Lesotho Thomas Motsoahae Thabane,

Jami’an soja a Lesotho sun musanta yunkurin juyin mulki a Lesotho. Suka ce sun dauki mataki ne kan wadansu ‘yan sanda da suke zaton suna kokarin samarwa wani bangaren siyasa makamai

Firai Ministan Lesotho ya tsere zuwa kasar Afrika ta Kudu domin gujewa abinda ya bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki a karamar masarautar.

Shaidu sun ce an ji karar harbe harben bindiga yau asabar a Maseru babban birnin kasar. Suka ce sojoji suna sintiri kan tituna, suka mamaye gine ginen gwamnati da kuma kewayen fadar gwamnati da Firai Minista Thomas Thabane ke zama.

Firai Minista Thomas Thabane yace abinda sojoji suka yi tamkar juyin mulki ne. ya bayyana cewa, ya tafi Afrika ta Kudu ne bayanda ya sami rahoton leken asiri cewa, sojoji suna neman hallaka shi.

A cikin hira da Muryar Amurka, Firai Minitan yace lamarin wani halin rashin da’a ne a rundunar.

Babban abin shine keta doka da oda da rundunar soja tayi. Sojojin suna bin tituna suna yiwa jama’a barazana, sojojin kuma suna fadi a fili cewa, suna nema su hallaka ni.

Firai Minista Thabane yace wani tsohon babban jami’in soji ne da gwamnati ta sauke daga mukaminsa madugun tashin hankalin. Yace yana da rahotannin leken asiri da ke nuni da cewa, tsohon kwamandan sojin yana da goyon bayan siyasa daga wadansu abokan aikinsa.

Mr. Thabane yace zai koma kasarsa da zarar ya hakikanta cewa ba za a kashe shi ba.

Jami’an soja a Lesotho sun musanta yunkurin juyin mulkin. Suka ce sun dauki mataki ne kan wadansu ‘yan sanda da suke zaton suna kokarin samarwa wani bangaren siyasa makamai.

Sun ce sojojin sun koma barikinsu kuma an sami zaman lafiya a kasar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG