Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Yi Bore A Kasar Ivory Coast


wannan boren na zuwa kwana daya ne bayan da wani mai magana da wawun Sojojin ya nemi gafarar Shugaban kasar akan boren watan janairu

A karo na biyu cikin wannan shekara, sojoji a kasar Ivory Coast sun rufe hanyoyi jiya juma’a a birane da dama na kasar domin yin zanga zangar nuna rashin amincewa akan rashin biyansu albashin su.

An fara tunzuri ne a Bouake, sa’anan ta bazu zuwa birnin Abidja da sauran biranen kasar. Anji karajin harbe harbe a baban sansani sojan kasar dake birnin Abija a yayinda sojoji suka ta harbi cikin iska.

Sojoji suna zanga zangar ce akan jinkirin da aka samu wajen biyansu alawus da gwamnati tayi musu alkawari bayan sunyi bore makamancin wannan a watan Janairu.

Gwamnantin kasar ta biya wani bangare na alawus din amma ta jinkira biyan sauran a saboda faduwar farshin coco, babar hajjar da kasar take sayarwa kasashen waje.

Anyi zanga zangar ce kwana daya, bayan wani mai magana da yawun soja ya nemi gafarar shugaban kasar Alassane Ouattara a saboda boren da sojoji suka yi a watan Janairu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG