Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama 'Yan Daba Kusan 1100 a Amurka


Wasu 'yan daba da aka kama.

A jiya Alhamis ne jami’an hukumar shige da ficen Amurka suka ce sun kawo karshen farautar ‘yan Daba da su ka kwashe makonni shida su na yi, inda suka kame kusan mutane 1100 wanda suke mambobin wasu munanan kungiyoyi.

Hukumomin shige da fice da Kwastam sunce mutanen da ake zargi ciki har da ‘yan kasashen waje su 445 daga kasashe 21, wanda suka hada da ‘yan yankin Latin Amurka da Asiya da Afirka da kuma Turai.

An kama kwayoyi masu yawan gaske da bindigogi da kuma kudi kusan Dala Dubu 500 a lokacin da akayi sumame a waus manyan birane dake nan Amurka.

Baki daya dai an kama mutane 1,378, cikin su kuwa an tabbatar da mutane 1,095 a matsayin ‘yan Daba.

Cikin ‘yan Daban kuwa akwai mambobin wasu fitattaun munanan kungiyoyi masu hatsarin gaske. Laifukan da suke aikatawa sun hada da safarar kwayoyi da makamai da mutane, sai kuma kisan kai da kuma zamba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG