Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Yi Ikirarin Kifar Da Gwamnatin Alpha Conde A Guinea


Alpha Conde

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito a ranar Lahadi cewa ya samu wani bidiyon shugaba Alpha Conde sanye da wata riga da wando da suka yamutse, yana zaune a wata kujera zagaye da sojoji.

Sojoji a kasar Guinea sun bayyana cewa sun kama Shugaba Alpha Conde sannan sun kawar da kundin tsarin mulkin kasar tare da rufe hanyoyin sufurin sama da kan iyakokin kasar.

Wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta nuna cewa an dakile wani hari da aka kai kan fadar shugaban kasar a birnin Conakry.

A dai watan Oktoba shugaban ya lashe zabe a karo na uku bayan da ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, abin da ya ba shi damar sake tsayawa takara duk da cewa ya kammala wa’adinsa na biyu.

Wannan mataki ya haifar da rudani da zanga-zanga a duk fadin kasar.

Yadda dakarun Guinea suke zagaya yankin birnin Conackry
Yadda dakarun Guinea suke zagaya yankin birnin Conackry

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito a ranar Lahadi cewa ya samu wani bidiyon shugaba Alpha Conde sanye da wata riga da wando da suka yamutse , yana zaune a wata kujera zagaye da sojoji.

Mamady Doumbouya, tsohon jami’i ya bayyana a kafar talabijin a ranar Lahadi nade da tutar kasar a jikinsa.

“Mun rusa gwamnati da kundin tsarin mulki,” Doumbouya ya ce. “Muna kira ga ‘yan uwanmu sojoji da su bi sahun mutane.”

Doumbouya ya bayyana cewa yadda ake tafiyar da gwamnati a karkace a kasar shi ne dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki.

Bayan wannan sanarwa, jama’a da dama sun bazama kan tituna suna murnar wannan juyin mulki da aka yi.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG