Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Afrika Ta Tsakiya Suna Yunkurin Hana Zaben Gobe Lahadi


Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Hadakar kungiyoyin ‘yan tawaye masu yaki da gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta fada a jiya Juma’a cewa zata dakatar da shirin tsagaita wuta na kwanaki uku kafin zaben karshen mako mai cike da tankiya.

Kungiyoyin ‘yan ta’addan sun kaddamar da wani farmaki a makon da ya gabata suna barazanar yin tattaki a babban burnin kasar Bangi, wani abin da gwamnati ta kwatanta da yunkurin juyin mulki, amma an taka musu burki da taimakon kasashen wajen.

Kungiyar hadakar ta Coalition of Patriots for Change CPC, ta sanar da takaitacciyar yarjejeniya kafin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a ranar Lahadi, da ake masa kallo wani babban jarrabawa ga kasar dake fama da tashin hankali.

Amma CPC ta fada a wata sanarwa a jiya Juma’a cewa zata dakatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta sa’o’i 72 da taba kanta kana ta fara gudanar da tattaki zuwa ga cimma babbar manufarta a cikin babban birnin kasar.

A cikin wata sanarwa da kungiyoyi biyu cikin kungiyoyi shida na hadaka ta CPC, suka tabbatarwa kamfanin dillancin labaran AFP cewa hadakar ta yanke shawarar yin gaba-da-gaba da gwamnatin mai taurin kunne mara kula da aiki.

‘Yan tawayen da suka sanya hannu a yarjejeniyar tsagaita wutar sun bukaci hukumomi suma su tsagaita a daidai wannan lokaci, suna kira ga shugaban kasa Faustin Archange Touadera da ya dakatar da zaben.

Amma mai magana da yawun gwamnati Ange-Maxime Kazagui ya yi watsi da batun tsagaita wutar a ranar Alhamis, mai fadin cewa “abin takaici ne saboda bamu ga wadannan mutane sun daina abin da suke yi ba.”

XS
SM
MD
LG