Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Ce Sun Lalata Jiragen Houthi Marasa Matuka A Tekun Bahar Ahmar Da Kuma Yemen


HMS Richmond shoots down two drones over Red Sea
HMS Richmond shoots down two drones over Red Sea

Rundunar sojin Amurka ta ce a ranar Lahadi dakarunta sun lalata wani jirgi mara matuki a yankin da ke hannun 'yan tawayen Houthi na Yemen da kuma wata hanyar jigilar kaya a tekun Bahar Ahmar.

Wannan dai shi ne al’amari na baya-bayan nan a cikin watanni da aka kwashe ana zaman dar-dar tsakanin 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Iran da Amurka.

Rundunar sojin Amurka ta ce jiragen da aka lalata da safiyar ranar Asabar, sun yi barazana ga sojojin Amurka da na hadin gwiwa da kuma jiragen ruwan 'yan kasuwa a yankin.

"Wadannan ayyuka sun zama dole don kare sojojin mu, tabbatar da 'yancin zirga zirga, da kuma tabbatar da tsaro ga Amurka, haɗin gwiwa, da jiragen ruwa na 'yan kasuwa," in ji CENTCOM.

Babu wani bayani daga 'yan tawayen Houthi, wadanda ke iko da yawancin arewaci da yammacin Yemen.

A handout picture released by the US Central Command (CENTCOM) on February 15, 2024, shows a US navy cutter next to a vessel reportedly carrying a shipment of Iranian weapons destined for Yemen's Huthi rebels which was seized on January 28.
A handout picture released by the US Central Command (CENTCOM) on February 15, 2024, shows a US navy cutter next to a vessel reportedly carrying a shipment of Iranian weapons destined for Yemen's Huthi rebels which was seized on January 28.

'Yan tawayen sun kaddamar da hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan jigilar kayayyaki a tekun na Bahar Ahmar a cikin watan Nuwamba. Sun kuma harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila, ko da yake sun gaza ko kuma an tare su.

'Yan tawayen dai sun bayyana yakin nasu a matsayin wani yunkuri na tursasawa Isra'ila ta kawo karshen yakin da take yi da kungiyar Hamas a zirin Gaza.

'Yan Houthi dai sun ci gaba da kai hare-hare duk da sama da watanni biyu na hare-haren da Amurka ta ke kai masu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG