Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin dake biyaya ga shuga Laurent Gbagbo sun cilla kwanson bamai bamai akan wata kasuwa har suka kashe mutane da dama


Wannan hoton wani mutum ne yake nuna shagon da aka kona a sakamakon fafatwa tsakanin sojojin dake biyaya ga shugaba Gbagbo da mayakan Ouattara mutumin da duniya tace shine ya lashe zaben shugaban kasar Ivory Coast

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sojoji masu yin biyayya ga shugaban da ya ki sauka daga kan mulki a kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, sun cilla kwanson bama-bamai a kan wata kasuwa a Abidjan, babbar cibiyar kasuwancin kasar, suka kashe mutane akalla 25.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sojoji masu yin biyayya ga shugaban da ya ki sauka daga kan mulki a kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, sun cilla kwanson bama-bamai a kan wata kasuwa a Abidjan, babbar cibiyar kasuwancin kasar, suka kashe mutane akalla 25. Ofishin ayyukan MDD a kasar Ivory Coast yace an raunata wasu mutanen su akalla 40 a hare-haren. An harba wadannan bama-bamai a wannan kasuwa dake unguwar Abobo, a cikin gundumar dake hannun mayaka masu yin biyayya ga shugaban kasar da duniya ta yi na’am da shi, Alassane Ouattara. A makon da ya shige, Kungiyar taraiyar kasashen Afrika ta amince da Mr. Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa na watan Nuwamba a Ivory Coast, ta kuma bi sahun kungiyar ECOWAS da MDD wajen yin kira ga Mr. Gabgbo da ya sauka. Mr. Ouattara ya yarda da shawarwarin Kungiyar kasashen Afrika na kyale Mr. Gbagbo ya sauka cikin lumana. Tsohon firayim ministan yayi tayin kafa gwamnatin hadin kan kasa da kafa hukumar bin diddigin gaskiya da sasantawa da kuma kafa rundunar sojojin da zata kunshi kowane bangare. Ya zuwa yanzu dai, Mr. Gbagbo yayi watsi da duk rokon da aka yi masa na ya sauka, kuma tashin hankalin da ya biyo bayan zabe ya haddasa fargabar sake barkewar yakin basasa a Ivory Coast. Tun fari a jiya alhamis, MDD ta ce yawan mutanen da suka mutu daga tashin hankalin da ya biyo bayan gardamar zabe ya karu zuwa akalla mutane 410.

XS
SM
MD
LG