Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sandan Zimbabwe Sun Hana Gangamin Taro


Zimbabwean PM and MDC President Morgan Tsvangirai speaks during a press conference in Harare (file photo).

‘Yan sanda a Zimbabwe sun hana gangamin taron da friminista Morgan Tsvangirai kuma jagoran ‘yan hamayya ya shirya yi ran Asabar. Rundunar ’Yan sandan ta Zimbabwe ta bada hujjar cewa basu da isassun ‘yan sandan da za’a tura domin kula da tsaro a lokacin gangamin taron.

Kamfanin dillancin labarai na Associated, ya bada rahoton cewa shaidun gani da ido sun tabbatar da ganin yadda ‘yan sanda suka rika korar magoya bayan Tsavangirai wasu ma har dukansu aka rika yi lokacin da suka isa wajen taron. Gangamin taron yazo dai dai da wanda shugaba Robert Mugabe ya shirya yi a kusa da inda Morgan Tsvangirai ya shiya yin nasa.

XS
SM
MD
LG