Accessibility links

Sojojin Najeriya Sun Cafke 'Yan Boko Haram a Maiduguri


Hafsan Sojojin Najeriya Janaral Minimah

Sojojin Najeriya na cigaba da fafatawa da 'yan Boko Haram inda suna kashe wasu da kuma cafke wasu

A kokarin kawo karshen fitinarda kungiyar Boko Haram ta tayar a arewa maso gabashin Najeriya sojojin kasar sun farma sansanonin 'yan tsageran kuma sun tarwatsasu lamarin da ya sa wasu sun arce zuwa birnin Maiduguri.

Farma sassanonin 'yan Boko Haram da sojoji suka yi ya karfafa matasan dake farautar 'yan kungiyar. Matasan da ake kira Civilian JTF suna cigaba da zakulo wasu daidaiku da suka arce daga gandun dajin sambisa inda suka kafa sansani da suke boyewa. Harin da sojojin suka kai ya yi sanadiyar mutuwar 'yan tsageran da dama.

Karshen makon jiya ne aka ga sojojin Najeriya dauke da manya manayan kayan yaki inda suka nufi dajin sambisa da yayi kaurin suna domin maharan sun mayarda shi sansaninsu. Daga dajin ne suke fitowa suna kai hari kan garuruwa da kauyuka. Bayan sun gama yin barna sai su koma cikin dajin.

Nasarar da sojojin suke samu ya sa matasan Civilian JTF kara himma wajen bin duk 'yan tsageran da suka sulalo cikin Maiduguri suka boye. Matasan suna cigaba da bincikar ababen hawa inda suke kame 'ya'yan kungiyar suna mikasu ga hukuma. Wasu ma da suka nufi tashoshin mota da nufin tserewa daga garin an kama su.

Mataimakin shugaban kwamitin dake horas da Civilian JTF kuma kwamishanan ma'aikatar shar'a Kaka Shehu Lawal ya kara haske kan abun da ya faru. Yace matasan suna sintiri da jami'an tsaro domin idan suka ga fuskar wanda ba dan garin ba ne sun sani sai su cafke su mikawa jami'an tsaro. Yace matasan suna samun nasara. Domin irin aikin da matasan suke yi gwamnati ta basu kayan aiki da saya masu motoci domin yin sintiri.

Ga karin bayani

XS
SM
MD
LG