Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Lahanta Abubakar Shekau Na Boko Haram A Harin Baya Bayan Nan


Abubakar Shekau na kungiyar Boko Haram da sojoji suka ce yanzu kam sun hallakashi

Daraktan watsa labarai na hedkwatar sojojin Najeriya Janar Rabe Abubakar yace suna da jiragen yakin dake tantance inda zasu kai hari ba tare da wani kuskure ba.

Jiragen na zamani suna da naurorin tantance abubuwan dake inda suke da nufin kai hari domin sanin takamaimai inda zasu kai farmaki.

Akan hare haren da 'yan kungiyar ke kaiwa kan wasu kauyukan jihar Borno Janar Abubakar yace ba wani abu ba ne illa son jawo hankulan 'yan jarida domin su ce har yanzu suna nan. Amma kungiyar ta san ta gama yawo.

Kwararre kan sojin mayakan sama Air Commore Ahmed Tijjani Baba Gamawa yace tsarin kai farmaki ta sama a Najeriya yanzu ya canza. Kayan da ake yayinsu a duniya su ne yanzu sojojin kasar suke aiki dasu. Sojojin sama suna da kayan aiki na zamani saboda haka babu mamaki su gano inda zasu kai farmaki kafin su aiwatar.

Ita ma hedkwatar sojin kasar Najeriya tace wani hari da suka kai a tungar 'yan Boko Haram ya lahanta jagoransu, Abubakar Shekau. Sojojin suna jin a wannan karon sun hallakashi.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG