Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kama Suka Lalata Wurin Harhada Bama-Bamai Na Boko Haram


Sojojin Najeriya Sun Lalata Wurin Hada Bama-Bamai Na Boko Haram A Sambisa
Sojojin Najeriya Sun Lalata Wurin Hada Bama-Bamai Na Boko Haram A Sambisa

Kakakin rundunar yaki da Boko Haram yace sojojin sama da na kasa sun fatattaki mayakan Boko Haram daga wata masana'antarsu ta harhada bama-bamai kusa da Camp Zairo suka lalata masana'antar baki daya.

Sojojin Najeriya dake yakar 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, sun ce sun gano wani makeken wurin harhada bama-bamai na kungiyar a cikin dajin Sambisa, a kusa da wurin nan mai suna Camp Zero, sun kuma lalata shi.

Mukaddashin Darektan yada labarai na Rundunar yaki da Boko Haram, da ake kira Operation Lafiya Dole, Kanar Onyema Nwachukwu, ya fada cikin wata sanarwar da ya bayar jiya laraba cewa sojojin na kasa dake samun tallafi daga mayakan sama, sun kutsa cikin wannan yanki shekaranjiya talata, inda suka yi ba-ta-kashi da mayakan Boko Haram dake gadin wannan wurin harhada bama-bamai.

Yace sojojin sun samu nasarar warware bama-baman da aka dana cikin motoci, tare da kama wannan masana'anta baki dayanta.

Abubuwan da sojojin suka gano sun hada da sundukai guda 88 na gas wadanda ake hada bam cikinsu, da kwamfutar hannu guda daya har ma da na'urar sanin inda mutum yake a duniya.

Haka kuma sun lalata babura guda 22 da kekuna 18.

Ko a cikin makon da ya shige ma, sai da sojojin na Najeriya suka sanar da kama wani babban sansanin 'yan Boko Haram a cikin dajin Sambisa, inda suka gano manyan motocin yaki da tankokina soja da 'yan Boko Haram din suka kwace daga hannun soja a shekarun baya.

To sai dai kuma a jiya laraba, shugaban bangare guda na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar da sabon bidiyo, inda a ciki yake ikirarin cewa wadannan motocin yaki da tankoki da sojoji ke cewa sun kwace, tarkacen yaki ne da su 'yan Boko Haram suka yi watsi da su shekaru uku da suka shige.

Sai dai kuma a cikin wannan bidiyon, an ji Abubakar Shekau yana fadin cewa da "wannan fitina, gara mutum ya je ya huta a lahira." Ba a san ko Shekau yana magana ne a kan hare-hare masu tsananin da sojojin kasa da na sama suke kaiwa a kan cibiyoyin 'yan Boko Haram a cikin 'yan kwanakin nan ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG