Dakarun Sudan ta Kudu sun ce sun kashe Kerbino Wol, shugaban wata sabuwar kungiyar ‘yan tawaye da ta bulla a kasar.
Kisan Wol na zuwa ne makonni kadan bayan da ya yi barazanar kifar da gwamnatin Shugaba Salva Kiir.
Kakakin sojojin kasar Manjo Janar Lul Ruai Koang, ya fadawa VOA cewa “an kashe Kerbino Wol Agok ne a ranar Lahadi da misalin karfe takwas na dare a wani kauye da ake kira Ayen Mayar da ke karamar hukumar Rumbek a jihar Lakes.”
An dai kwashe kwanaki sojojin kasar ta Sudan ta Kudu suna fafatawa da mayakan sabuwar kungiyar ‘yan tawayen a cewar kakakin sojin kasar.
Ya kara da cewa an kashe mayakan Wol uku da wasu fararen hula biyu yayin wannan arangamar.
Kusan makonni biyu da suka gabata ne Wol ya ayyana tawayensa inda ya ce zai yaki gwamnatin shugaba Kiir ya kuma hambarar da ita daga kan mulki.

Wasu dakarun Sudan ta Kudu a bakin daga a kuso da garin Kuek, a arewacin jihar Upper Nile a Sudan ta Kudu
Photo: AP
WASHINGTON D.C. —
Facebook Forum