Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Syria Sunyi Amfani Da Bama Baman Kusa?


Hotunan wasu msu zanga zangar nuna kyamar gwamnati dake saye da sutura launin tutar 'yan tawaye.

Masu neman chanji a kasar Syria sunce sojan kasar sun saki bama-bamman kusoshi akan mutanen da suka fito yau Jumu’a suna zanga-zangar nuna tsanuwar gwamnati.

Masu neman chanji a kasar Syria sunce sojan kasar sun saki bama-bamman kusoshi akan mutanen da suka fito yau Jumu’a suna zanga-zangar nuna tsanuwar gwamnati, kwana daya bayanda ‘yan kwamitin gani-da-ido na kasashen Larabawa suka kamalla ziyarar wasu daga cikin wuraren da ake riginginmun.

Cibiyar ‘yan adawa ta “Observatory” tace anyi anfani da wadanan bama-bamman ne wajen tarwatsa gungun irin wadanan mutanen da suka yi kwamba a unguwar Douma dake Damascus, babban birnin kasar.

Cibiyar tace masu zamga-zangar kuma sun rama ta hanyar jifar sojan da duwatsu. ‘Yan adawar kuma sunce an kashe mutane 5 a Daraa yayinda wasu 4 kuma suka rasa rayukkansu a cikin farmakin da sojan gwamnatin suka kai kusa da kan iyaka da Lebanon.

XS
SM
MD
LG