Accessibility links

Ministocin Harkokin Waje Kasashen Larabawa Suna Taro A Alkahira Kan Rikici A Syria

  • Aliyu Imam

Daga hagu, babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Nabil al-Araby, da ministan harkokin wajen Qatar,r Hamad bin Jassim a taron kungiyar a Alkahira.

Yau lahadi ministocin harkokin waje na kasashe dake kungiyar hada kan larabawa suke taro da nufin sake duba aikin wakilanta masu sa ido a Syria.

Yau lahadi ministocin harkokin waje na kasashe dake kungiyar hada kan larabawa suke taro da nufin sake duba aikin wakilanta masu sa ido a Syria, ganin duk da kasancewarsu a kasar, bai hana mummunar matakan gwamnatin kasar na murkushe farar hula masu zanga zanga.

Ministocin sun hallara ne a birnin Alkahira kwana daya bayan da aka sami rahotannin arangamomi sun halaka akalla mutane ashirin da daya a duk fadin Syria, kuma kwanaki biyu bayan tashin wani bam a Damascus, wadda ya hallaka mutane ashirin da shida.Haka kuma ‘yan hamayya suna zargin gwamnati da kashe farar hula 17 a gwabzawar da aka yi ranar jumma’a.

Ministocin zasu yi shawara kan ko su nemawa shirin nasu taimakon MDD ganin aikin wakilan bai sassauta tarzomar da ake yi kasar ba duk cewa wakilan suna can mako biyu kenan.

Wani dandalin dake goyon bayan kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya a fadin Duniya baki daya da ake kira AVAAZ, yace kusan mutane dubu bakwai ne aka kashe a kasar ta sham tun fara bore a cikin watan Maris na bara. Dandalin yace ya gaskanta wan adadin ne bayan tuntubar da majiyoyi da dama cikin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tana kyasta an kashe akalla mutane dubu biyar a wan nan boren. Yayin da gwamnatin Syrian take aza laifin kashe kashen kan ‘yan ta’adda wadan da take zargin sun kashe jami’an tsaro dubu biyu.

XS
SM
MD
LG