Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soludo Ya Sanya Dokar Hana Fita a Kananan Hukumomin Anambra 7


Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo (Hoto: Facebook/Charles Soludo)
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo (Hoto: Facebook/Charles Soludo)

Gwamnatin jihar Anambra ta saka dokar Hana fita a wasu kananaan hukumomi 7 dake jihar ta Anambra sakamakon tsanantar kashe kashe a jihar.

Gwamnan jihar Anambra Farfesa Chukwuma Soludo a ranar Laraba ya sanya dokar hana fita a kananan hukumomi bakwai na jihar.

A wani jawabi da ya yi a fadin jihar a Awka, Soludo ya ce dokar za ta fara aiki ne a ranar Alhamis daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

Hakazalika ya kuma haramtawa babura, kekunan a dai-daita sahu na kasuwanci da ake kira Keke Napep, da motocin bus-bus daga aiki a kananan hukumomin da abin ya shafa a ranar Litinin har sai an daina ba da umarnin zama a gidan ya kare.

“Daga ranar Alhamis, 26 ga Mayu, 2022, an sanya dokar ta-baci daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kan babura (Okada), Keke, da motocin bas a cikin Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi North, Nnewi ta Kudu, Ogbaru , Kananan Hukumomin Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu,” inji shi.

"Har ila yau an bada sanarwa kuma, na hana babura, Keke, da motocin bus-bus yin aiki a wadannan kananan hukumomin a ranar Litinin har sai lokacin da umarnin zama a gidan ya tsaya gaba daya."

Gwamnan ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su ba shi hadin kai domin cimma burinsa na ganin jihar Anambra ta zama kasa mai albarka da wadata.

“An umurci matasan kowace al’umma a shiyyar da su taimaka wa jami’an tsaro wajen aiwatar da wannan manufa kuma an umurce su da su kama duk wani babur ko keken adai-daita sahu nan take,” inji shi.

“Ya kamata ‘yan banga na gari su kai rahoton irin wadannan babura ko masu keke (Keke) nan take, kuma gwamnati za ta kwace su kuma za a gurfanar da mai shi a gaban kuliya.

“Dole ne shugabannin kungiyar Okada, da na Keke, da ma na bas su dauki nauyin kai rahoton mambobinsu da ke da hannu wajen aikata laifuka. Za mu sake duba hakan bayan makonni biyu, kuma idan mambobin wadannan kungiyoyin suka ci gaba da aikata laifuka, gwamnati ba ta da wani zabi illa ko dai ta ruguza kungiyoyin ko kuma ta haramta su a cikin jihar yadda ya kamata.”

Rahoton Wakilin Muryar Amurka Abubakar Lamido Sakkwato da karin bayani daga rahoton ChannelsTV.

Saurari karin bayanin rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
XS
SM
MD
LG