Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOMALIA: Al-Shabab ta Kashe Sojojin Kungiyar Kasashen Afirka


Wani mayakin al-Shabab a sansanin da suka kai hari

A wani mummunan hari da kungiyar al-Shabab ta kai kan sojojin kungiyar kasashen Afirka, wajen su 19 suka kwanta dama

Akalla dakarun hadin gwiwa na Kungiyar Kasashen Afirka 19 kungiya Al Shabab ta kashe a Somalia a yau Talata, a wani harin bam da aka kai cikin wata mota da kuma wani harin na dabdan a sansanin sojin.

Wani babban jam’in kasar ta Somaliya ne ya gayawa Muryar Amurka adadin sojojin da aka kashe, ya kuma ce ‘yan kungiyar ta Al Shabab da ke da alaka da Al Qaeda, sun yi awun gaba da wasu dakarun hadin gwiwa na kungiyar tarayyar Afrika da yawansu ya kusa 19.

Kungiyar dai ta yi ikrarin kashe dakarun da dama a wannan hari na sansanin sojin da ke Jannaale, mai tazarar nisan kilomita 120 kudu da Maogadishu, babban birnin kasar ta Somaliya.

Kungiyar dakarun tarayyar Afrika ta AMISOM, ta musanta wannan ikrari na Al Shabab.

Sai dai wadanda suka shaida lamarin sun ce, dakarun sun arce, domin kaucewa harin kungiyar ta Al- Shabab.

XS
SM
MD
LG