Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOMALIYA: Yan Ta'adda Sun Kashe Jami'an Tsaron 12 A Jihar Galmudug


Harin an kai shi ne a kusa da kauyen El-Dhere, mai nisan kilomita 28 yamma da birnin Dhusamareb, a lokacin da jami’an tsaron suka fita wani aiki a cewar jami’an.

Shi dai birnin Dhusamareb na tazarar kilomita 510 yamma da Mogadishu, babban birnin kasar taSomaliya.

Dakarun Sojan Somaliya
Dakarun Sojan Somaliya


Babban jami’in tattara bayanan sirri a garin na Dhusamareb, Manjo Abdirashid Abdinur Qoje, na daya daga cikin wadanda suka mutu, a cewar ministan yada labarai, Ahmed Shire Falagle, wanda ya tabbatarwa da Muryar Amurka aukuwar harin.

XS
SM
MD
LG