Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SUDAN TA KUDU: An Cimma Yarjejeniya Kan Rikicin Kasar


Taron IGAD na samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya amince zai rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya dake da nufin kawo karshen yakin basasar watanni 20 da kasar shi ta ke fama da shi.

Wata wasika da aka aiko wa shirin Talabijin na In Focus, wanda ke mayar da hankali akan Sudan ta Kudu da Muryar Amurka take gabatarwa da harshen turanci, Kungiyar kasashen gabashin Afirka ko IGAD a takaice ta bayyana cewa za’a saka wa yarjejeniyar hannu a birnin Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.

Kungiyar IGAD itace ta jagoranci neman sulhu tsakanin gwamnatin Mr. Kiir, da ‘yan tawayen da tsohon mataimakin Shugaban kasa Riek Machar ke jagoranta.

Machar ya sanya wa yarjejeniyar hannu a birnin Addis Ababa ran 17 ga watan Agusta, amma shugaban Sudan ta Kudu yayi watsi da ita, inda ya ce yarjejeniyar baza ta tabbatar da dorarriyar zaman lafiya ba.

Kasar Amurka ta yi barazanar kakabawa shuwagabanin dake hammaya su biyu takunkumai idan har basu samu cigaba ba, a yunkurin kawo karshen wannan yaki. Rigingimun Sudan ta Kudu sun raba mutane kusan miliyan 2 da dubu dari 2 daga muhallansu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG