Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu: An kai hari a sansanin dake karkashin Majalisar Dinkin Duniya


Shugaban 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar wanda yanzu shi ne kuma mataimakin shugaban kasa

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 25 aka kashe yayin da aka jikkata wasu 120 a lokacin da aka kai wani hari kan sasanin fararen hula da ke karkashin kulawar Majalisar, a Malakal a watan da ya gabata a Sudan ta Kudu.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ayyukan jin kai ne ya fitar da sabon adadin a yau Juma’a, makwanni biyu bayan harin da aka kai a ranar 17 da 18 ga watan Fabrairu a sansanin da ke dauke da ‘yan gudun hijra dubu 47.

Rahoton da ofishin jin kan ya fitar ya kara da cewa baya ga mutane 25 da suka mutu da 120 da suka jikkata, an barnata matsugunan iyalai dubu 3,700, da kuma wuraren shan magani da tankunan ruwan sha da makarantu.

Ofishin na Majalisa Dinkin Duniya ya kara da cewa, akwai hujjojin da suka nuna cewa mayakan kungiyar SPLA ne suka shiga sansanin suka bude wuta akan fararen hula.

Yanzu haka hukumomin sun dukufa ne domin ganin an maido da ayyukan jin kai yadda su ke a sansanin, yayin da ake ci gaba da rarraba kayayyakin more rayuwa ga dubban ‘yan gudun hijrar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG