Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Na Gaban Kasashen da Suka Fi Hallaka 'Yanjarida A Shekarar 2016


Shugabannin kasar Sudan ta Kudu

Hukumar kare hakkin 'yan jarida ta duniya tace kashi casa'in da biyar cikin 'yan jaridan da ake kashewa ana kashesu ne a kasashensu na asali ba tare da yi masu shari'a

Kungiyar kare hakkin ‘Yanjaridu ta Duniya (C-P-J) tace kashi 95% na ‘yanjaridun da aka hallaka a kasashen duniya daba-daban a cikin shekaru 10 da suka gabata, an hallaka su ne a cikin kasashensu na asali – amma kuma sau da yawa ba akan hukunta masu kisan nasu ba, abinda kungiyar ta CPJ tace yana daya daga cikin abubuwan da suka dade suna zaman babban kalubale a wurin ‘yanjaridun.

Elizabeth Witchel, marubuciyar rahoton musamman kan wannan lamarin, tace kasar Sudan ta Kudu na daga cikin kasashen dake sahun gaba wajen hallaka ‘yanjaridu a wannan shekarar ta 2016, inda tace ba wai sojan gwamnati ne kadai ke yawan kai hari akan manema labaran ba, har da kungiyoyin ‘yan banga sun sha auna ‘yanjaridu.

To amma Kasar da itace kan sahun gaba fiyeda da kowace kasa wajen kuntatawa ‘yanjarida a duniya itace Somalia, a cewar rahoton, inda galibi ta hannun kungiyar ta’addanci ta al-Shebab manema labaran suka fi yawan asaran rayukkansu. Kasashen Iraq da Syria ne suka zo na biyu da ta ukku a wannan matsalar ta gallazawa ‘yanjarida a duniya.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG