Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Ta Fara Sasanta Kasar Sudan


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta nemi ta sasanta tsakanin gwamnatin sojin Sudan da ‘yan adawa, a matsayin ramawa Sudan rawar gani da ta taka a lokacin tattaunawar zaman lafiyar Sudan ta Kudu a bara.

Wani minista a ofishin shugaba Salva Kiir, yace shugaban kasar ya nuna damuwarsa ga abin dake faruwa a Sudan kuma yana kira ga bamgarorin biyu su kafa gwamnatin wucin gadi da wuri.

Minista a fadar shugaban Sudan ta Kudu, Mayiik Deng yana cikin tawagar mutane hudu da mai ba shugaba Kiir shawara a kan tsaro ya jagoranci zuwa Tut Galuak inda suka kammala ziyarar kwanaki biyu da suka kai a birnin Khartoum a jiya Juma’a.

Deng yace tawagar ta isar da sakon zaman lafiya ne ga shugabannin Sudan tare da yin kira gare su su nemi hanya mafi inganci su sasanta tsakanin jami’iyyun adawa da ita gwamnatin wucin gadin sojojin kasar.

Yayin da suke Khartoum, Deng yace tawagar ta gana da sojojin kasar da shugabannin ‘yan adawa a laokaci dabam daban, yana fada musu cewa jami’an Sudan ta Kudu suna da cikakken kwarewar da zasu shiga tsakani domin tabbatar da zaman lafiya a Sudan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG