Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunwa Na Dab Da Hallaka Mutane Dubu 30 A Sudan Ta Kudu


Ana digawa wani karamin Yaro dan Sudan Ta kudu magarin rigakafi

Rahottani daga kasar Sudan ta Kudu na cewa yanzu haka akwai mutane sun kai 30,000 da ke dab da fuskantar halaka daga matsanaciyar yunwa ta innali-Lah dake addabar wannan kasar

Wani rahoton dake da daurin gindin hukumomin samarda abinci na Majalisar Dinkin Duniya yace, musamman, akwai wasu yankunan kananan hukumomi guda hudu dake kasar da, idan ba agajin abinci aka kai musu ba kafin karshen shekarar nan, Allah kadai Ya san mutanen da zasu tagayyara a sanadin masifar karancin abincin da zasu fuskanta.

Rahoton yace kusan mutane milyan hudu ko kace sulusi daya na daukacin dukkan mutanen wannan kasa ta Sudan ta Kudu ke ciki wannan mawuyacin hali na yunwa a jihohin Unity, Jonglei da Upper Nile.

Wata sanarwar hadin gwiwa da wasu hukumomi ukku na MDD da suka hada da Hukumar kula da yara ta UNICEF, da Hukumar Samarda Abinci ta WFP da kuma Hukumar Bunkasa Aiyukan Gona ta FAO, duk sun yi kira akan rukunonin mutanen dake yaki da juna a kasar Sudan ta Kudu din da su bari, su bude hanyoyi don a samu a shiga a kaiwa mutane kayan cimaka na agaji.

Tun cikin watan Disambar 2013 ake gwabza yaki tsakanin sojan gwamnati da mayakan ‘yantawaye dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar, Rick Machar, yakin da ya tada mutane kamar milyan 2.6 daga gidajensu na zama.

XS
SM
MD
LG