Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sufeta Janar Na ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sa Ayi Binciken Harin Da Aka Kai Kan Tawagar Atiku A Jihar Borno


IGP Alkali Baba Usman.
IGP Alkali Baba Usman.

Tunda farko dai babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi zargin cewa gungun ‘yan bangar siyasa sun kai wa tawagar dan takararta hari a birnin Maiduguri jim kadan bayan wani gangamin kamfe inda aka jikkata magoya baya har arba'in da bakwai tare da lalata motocin da ke cikin tawagar.

BORNO, NIGERIA - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara binciken harin da ake zargin cewa wasu ‘yan bangar siyasa sun kai kan tawagar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ‘dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, a birnin maiduguri na Jihar Borno.

Amma rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta karyata maganar inda mai magana da yawun rundunar ya ce zargin bai da tushe balle makama, kuma kakakin ‘yan sandan na Jihar Borno Kamilu Sharubutu ya ce zargin wani yunkurin haddasa rudani ne a Jihar.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

To amma cikin wani abu mai kama da martani mai marwara, Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya amince cewa lalle an kai wannan farmaki inda ya ci gaba da cewa ''Lallai abin da ya faru a Borno ya faru, kakakin ‘yan sandan na Borno ya yi gaggawar yin martani akan batun, don haka za a yi bincike na kwakwaf don gano abin da ya faru da zummar hana aukuwar haka nan gaba''

Tuni kuma jam'iyyar PDP ta yi na'am da wannan mataki, inda mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya nemi lallai a yi bincike na hakika kuma a ladabtar da duk masu hannu cikin wannan lamari.

Saurari cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina:

Sufeta Janar Na ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sa Ayi Binciken Harin Da Aka Kai Kan Twawagar Atiku A Jihar Borno.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

XS
SM
MD
LG