Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sukar Da Trump Ya Yiwa Bangaren Shari'a Abin Takaicine - Gorsuch


Shugaban Amurka Donald Trump

Neil Gorsuch wato mutumin da shugaban Amurka Donald Trump ya zaba a matsayin wanda zai cike gurbi a kotun kolin kasar, ya ce sukar da Trump din ya yiwa bangaren shari’ar kasar abu ne mai kashewa mutumin jiki, kuma abin takaici ne.

Gorsuch ya yi wannan furuci ne a wurin wata tattauanawa da wani wakilin jami’iyar Democrat a majalisar dattawa Richard Blumenthal jiya Laraba.


An yiwa Gorsuch tambaya ne a kan sakon Twitter da shugaba Trump ya aika inda ya kira wani alkalin lardi James Robart wanda ya dakatar da umarnin shugaban kasa na haramtawa 'yan wasu kasashe bakwai da galibinsu musulmi shiga Amurka da cewar “ana kiransa alkali”.


Trump ya ce Amurkawa su zargi Robart da tsarin shari’ar kasar idan wani mugun abu ya faru a kasar mai nasaba da ta’addanci.

XS
SM
MD
LG