Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sumbata Ka Iya Kara Yaduwar Cutar Zika


Wasu Ma'aurata Suna Sumbatar Juna
Wasu Ma'aurata Suna Sumbatar Juna

Hukumomi a Brazil sun ce an samu burbushi ko kuma samfurin kwayar cutar Zika a yawu da kuma fitsarin masu dauke da cutar.

Yayin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai a jiya Juma’a, shugaban cibiyar bincike ta Oswaldo Cruz, Paulo Gadelha, ya ce akwai yuwuwar sumbata ta baki-da-baki ta iya kara yaduwar cutar ta Zika.

Sai dai ya ce hakan ba wai yana ba da shawara a fitar da wani tsari na hana mutane sumbatar junansu ba ne.

Masana kimiyya a wannan cibiya na kokari ne su gano ko nau’ukan ruwan da ake samun a jikin dan Adam kamar su yawu da fitsari da sauransu, za suya iya yada cutar ta Zika.

Wannan sabon bincike na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Brazil ta shiga lokacin wasu shagugulan biki da mutane ke sumbatar duk wanda suka hadu da shi a wajen wannan biki, wanda da ake gudanarwar a kan tituna kasar, wato koda ba ka san mutum ba.

A daya bangaren kuma, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ba da shawarar kada asibitoci su karbi tallafin jini daga mutanen da suka dawo daga kasashen da ke fama da cutar ta Zika.

Cutar wacce ta fi kamari a Brazil, kan shafi masu juna biyu.

XS
SM
MD
LG