Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria Ta Harbo Wani Jirgin Kasar Rasha


Wani Jirgin Kasar Rasha
Wani Jirgin Kasar Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana harbo jirgin sojin Rasha da kasar Syria tayi a matsayin jerin hadura, abinda ya yayafa ruwa kan lamarin da zai iya kawo tashin hankali da Isra’ila.

Mutane goma sha biyar dake cikin jirgin Rashan suka mutu lokacin da Syria ta harbo shi, yayinda take maida martani kan harin roka da Isra’ila ta kai.

Ministan tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu, ya shaidawa takwaran aikinsa na kasar Isra’ila Avigdor Leiberman cewa, alhakin lsra’ila ne kuma Rasha tana da ‘yancin maida martani.

Sai dai Putin ya shiga Tsakani ya bayyana lamarin a matsayin jerin hadura da suka zama abin takaici. Yace Rasha zata maida martani ta wajen daukar Karin matakan kare jami’anta da kuma kaddarorin Syria. Ya kara da cewa, kowa zai ga irin matakan da za a dauka.

Pirayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana jimamin rasa rayukan 'yan kasar Rashan, ya kuma dorawa Syria alhakin.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG